Ƙungiyar Kare Haƙƙin Jama’a da Kula da Al’amuran Tattalin Arziki (SERAP), ta bai wa Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN), Olayemi Cardoso, kwanaki bakwai da ya fitar da bayanai kan Naira Tiriliyan 3 na kuɗaɗen al’umma da ake zargin sun yi batan dabo.
Ƙungiyar ta bayyana cewa wannan lamari na zuwa ne bayan wani rahoton Babban Ma’ajin Kasa na shekara ta 2022, wanda ya buƙaci CBN ya bayyana inda kuɗaɗen suka shiga.
Rahoton ya nuna akwai matsalar ɓacewar rarar kudi da basukan da ba a biya ba da kuma kwangiloli masu cike da ayoyin tambaya.
SERAP ta ce CBN ya gaza tura sama da naira triliyan 1 da biliyan 440 na rarar kudi na gwamnatin tarayya zuwa asusun kuɗaɗen shiga na bai ɗaya.
A sanarwar da ta fitar, SERAP ta lura cewa CBN bai karɓo sama da naira biliyan 700 ba na basussukan da kuɗaden kai dauki da aka bayar tsakanin 2018 zuwa Mayun 2022 ba.
Haka kuma CBN ya bayar da kwangiloli 43, na sama da Naira biliyan 189, sai dai ƴan kwangilar sun yi jinkiri da gangan inda daga baya suka buƙaci a sauya farashin kwangilar wanda ya kai ga biyan kuɗi fiye da Naira biliyan 9 ba bisa ƙa’ida ba.
Tana kuma fargabar za a iya karkatar da waɗannan kudaɗen don haka ne ta nemi a gaggauta dawo da su baitul malin gwamnati, ko ta ɗauki matakin shari’ah.











