Home Labarai Rundunar ‘yan sanda Abuja ta Musanta yunkurin hallaka Lt. Ahmed Yerima

Rundunar ‘yan sanda Abuja ta Musanta yunkurin hallaka Lt. Ahmed Yerima

Rundunar ƴansandan birnin Abuja, ta musanta wani iƙirari dake cewa wasu ‘yan bindiga sun yi yunkurin hallaka Laftanar Ahmed Yerima.

Wannan na cikin wata sanarwa da rundunar ƴansandan Najeriya, reshen birnin na Abuja ta fitar ta hannun kakakinta, SP Josephine Adeh,  in da ta ce babu inda aka samu irin wannan iƙirari, labara ne kawai da bashi da tushe ballantana makama.

Da yammacin ranar Lahadi ne rahotonin yunƙurin kashe Laftanar Ahmed Yerima – matashin sojan da ya yi sa-in-sa da ministan Abuja, Nyesom Wike a makon da ya gabata – suka cika shafukan sada zumunta.

Rahotonnin sun yi iƙirarin cewa wasu matasa ne da ba a san ko su wane ne ba suka yi yunƙurin halaka sojan ruwan a Abuja, babban birnin ƙasar.

”Rundunar ƴansanda reshen Abuja ta lura da abubuwan da ke yawo a shafukan sada zumunta, da ke zargin an yi yunƙurin kashe Lt. Ahmed Yerima.

“Rundunar na son bayyana wa al’umma cewa ba mu samu wasu bayanai game da iƙirarin da ake yaɗawa ba ɗaukacin yankin Babban Birnin Tarayya,” in ji SP Josephine Adeh.

Daga bisani rundunar ‘yansandan ta shawarci al’umma su guji yaɗa labaran da ba su da tabbaci a kansu, saboda a cewarta babu abin da hakan ke haifarwa sai tayar da hankula.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Darakta Janar na NITDA ya yi Kira da a Hada Hannu Kan Tsarin AI a Taron Manyan ShugabanniƳancin Sanin Gaskiya: Bayani Game da Tsarin Gudanar da Harkokin Sadarwa na Najeriya Daga Franklyn Ginger-EkeHOTO: NSCDC ta Tsare Jami'ai 24 Kan Mutuwar Masu Hakar Ma'adinai a TsareShirin Tallafin Mai: Atiku ya yi Watsi da Gaskiyar Magana – APCGwamnatin Tarayya ta Inganta Samar da Abinci ta Hanyar Shirin AgriShield na ONSA Daga Chido OnumahAtiku ya yi Tambaya Kan Rashin Zuwa UNGA a Karo na Uku da Tinubu ya yi, ya Nemi Karin BayaniFalconets ta Fice Daga Gasar Cin Kofin Duniya ta Mata Ƴan Kasa da Shekaru 20 Bayan Colombia ta Sha Kashi a Wasan KarsheMatawalle Ya Nemi Tallafin Czech Don Samar da Alburusan DICON da Canja FasahaRundunar Sojojin Najeriya Ta Tallafa wa Iyalan Sojojin Gambia da Suka MutuFilato: Sojoji Sun Kama Masu Garkuwa 11, Sun Kwato MakamaiOPHK ta yi Bayani Kan Rahoton Amnesty na 2016 Dangane da Mutuwar da Ake Zargi a Barkin Giwa2027: Sama da Mambobin Jam'iyyar NDC 6,000 Sun Sauya Sheka Zuwa PDP a EnuguKwankwaso ya Nuna Aniyar Yin Sulhu da Gwamna YusufYadda Hon. Hudu Kanje Ya Sake Fasalin Jagorancin Cigaban Kasa Daga Mika'il Ja'afarƳan Sanda Sun Kama Mutane 300 a Farmakin Wuraren da Ake Aikata Laifuka a FCT Sun Kwace Wukake, Bindigar Wasa, da Wiwi
X whatsapp