Home AFIRKA ECOWAS ta dakatar da Guinea Bissau sakamakon juyin mulkin Sojoji

ECOWAS ta dakatar da Guinea Bissau sakamakon juyin mulkin Sojoji

Ƙungiyar ECOWAS ta dakatar da Guinea-Bissau kwanaki biyu bayan juyin mulkin da ya kawo ƙarshen gwamnatin shugaba Umaro Sissoco Embalo daidai lokacin da ake dakon sakamakon zaɓen da shugaban ke neman tazarce.

ECOWAS ta bayyana juyin mulkin na Guinea Bissau a matsayin babbar barazana ga tsarin dimokaraɗiyya a ƙasar ta yammacin Afrika.

Cikin matsayar da wannan taro na ECOWAS ya cimma, akwai dakatar da wannan ƙungiyar da kuma matsa mata lamba don ganin ta koma mulkin farar hula don tabbatar da demokraɗiyya.

Tuni dai hamɓararren shugaban na Guinea Bissau, Umaro Sissoco Embalo ya sauka a ƙasar Senegal a wani jirgi na musamman jiya Alhamis, biyo bayan shiga tsakani da ƙungiyar ECOWAS ta yi, kamar yadda ma’aikatar harkokin wajen Senegal ta bayyana.

Wannan ne juyin mulki na 9 da ake fuskanta a ƙasashen yammaci da Tsakiyar Afirka cikin shekaru biyar da suka gabata.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Gwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige FubaraMasu haƙar ma’adinai 33 sun mutu sakamakon gubar sinadarin carbon a FilatoSojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta'addanciGwamnatin Najeriya da gwamnonin APC sun bai wa ƴan kasuwar Singer tallafin biliyan 8Kwankwasiyya ta yi martani kan matakin majalisar Amurka na hukunta KwankwasoSojojin Najeriya sun daƙile hare-haren mayaƙan ISWAP a BornoFarfesa Abdullahi Pakistan ya bayyana dalilinsa na ajiye shugaban Hukumar NAHCONMajalisar Najeriya ta kafa kwamitin nazari kan gyaran dokar zaɓeRundunar sojin Najeriya ta tura dakaru na musamman zuwa Filato don daƙile ƴanbindigaMajalisar Dinkin Duniya da Turkiya sun yi Alla-wadai da harin da aka kai KwaraAmurka ka iya sake kai Hari Nijeriya muddin aka ci gaba da kashe kiristoci- TrumpAmurka ka iya sake kai hari Nijeriya muddin aka ci gaba da kashe kiristoci
X whatsapp