Kungiyar kare hakkin dan Adam ta Amnesty international tayi Allah wadai da abin da ta kira tauye hakkin dan adam da rundunar ‘yan sanda Nijeriya ke ci gaba da yiwa tsohon shugaban hukumar yaki da cin hanci da karbar korafe korafe ta jihar Kano Muhuyi magaji Rimin Gado.
Read Also:
Ta cikin wani sautin murya da shugaban hukumar gudanarwa ta kungiyar ya aikewa PRNigeria Hausa, ya bayyana cewa kungiyar ta yi tofin alatsine kan yadda ake ci gaba da musgunawa gami da tauyi hakkin Muhuyi duk dace doka bata bawa ‘yan sandan damar kama shi ba, haka kuma babu wata kotu da ta bada umarnin yin kamun.
Kungiyar ta bukaci rundunar ‘yan sandan Nijeriya da ta gaggauata sakin Muhuyi tare kuma da daina cin zarafinsa da sauran Al’ummar Nijeriya.
Ba dai wannan ne karon barko da dakarun ‘yan sandan ke yiwa Muhuyi wannan kamu ba, duk da cewa ana kallon hakan na da nasaba da takun saka da yake fuskanta da wasu ‘yan siyasa a jihar Kano.









