Jagoran jam’iyyar NNPP, Rabiu Musa Kwankwaso, ya nuna matuƙar damuwa kan yadda matsalar tsaro ke ta ’kara munana a Najeriya, yana mai gargaɗin cewa matsalolin tsaro da ke faruwa yanzu na neman ya fi ƙarfin gwamnati.
Ya bayyana hakan ne a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X.
Kwankwaso, wanda ya taɓa zama gwamnan Kano, ya ce alamu na nuna cewa matsalolin tsaro da ke faruwa yanzu ka iya zama babbar barazana ga haɗin kai da kwanciyar hankalin ƙasa.
A cikin saƙonsa, ya ce: “Dukkan alamu na nuna cewa rashin tsaro na neman ya fi ƙarfin gwamnatin. Wannan na bayyana a yadda take barin jihohi su kafa ƙungiyoyin tsaro na ƴan sa kai ba tare da horo na musamman ba.”
“Wannan mataki, ko da an yi shi da kyakkyawar niyya, ya haddasa yaɗuwar ƙananan makamai da manyan makamai a faɗin ƙasa.” in ji shi.
Kwankwaso ya kuma nuna damuwa kan yadda ake samun ƙaruwa a tsangwama da azabtar da ’yan Najeriya musamman daga wasu yankuna.
Ya ce “wasu ’yan siyasa ma sun fara amfani inda ya ƙara da cewa kalaman ƙiyayya a kafofin sada zumunta na ƙara rura wutar rikici da raba kan al’umma.
Kwankwaso ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta hanzarta ɗaukar mataki kafin lamura su lalace gaba ɗaya.









