Za mu ci gaba da kamen masu bakin gilashin mota – Yan sanda

Ƴansandan Najeriya sun sanar da cewa za su ci gaba da tilasta bin dokar mallakar lasisin amfani da gilashin mota mai duhu ko kuma su ci gaba da kame daga 2 ga Janairu 2026, abin da ya janyo suka daga ƙungiyar lauyoyin Najeriya (NBA), wadda ta bayyana matakin a matsayin saɓa wa hukuncin kotu da kuma tauye doka.

Wannan sanarwa ta fito ne daga CSP Benjamin Hundeyin, jami’in hulɗa da jama’a na hukumar ƴan Sanda, a ranar 15 ga Disamba 2025.

NBA ta bayyana cewa matakin ƴansandan ya saɓawa hukuncin da kotu ta yanke inda ta dakatar da aiwatar da dokar har sai an gama shari’ar ƙarar ƴansandanda aka shigar a gabanta na ƙalubalantar halaccin dokar.

Lauyoyi sun yi gargadi cewa wannan mataki zai ƙara nauyi ne ga talakawa, kuma zai iya jawo cin hanci da rashawa.

Wannan lamarin ya fara ne a watan Afrilu 2025 lokacin da rundunar ƴansandan Najeriya ta shigo da dokar mallakar lasisin gilashin mota mai duhu, wacce ta bukaci ‘yan Najeriya su yi rijista ta intanet domin samun lasisi inda aka tsara fara aiwatar da dokar a ranar 1 ga Yuni 2025, daga baya aka ɗage zuwa 2 ga Oktoba saboda korafe-korafe da dama daga jama’a.

NBA ta buƙaci ƴansandan da su dakatar da duk wani mataki na ci gaba da aiwatar da dokar har sai kotu ta yanke hukunci na ƙarshe.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com