Majalisa ta amince da naɗin sabbin jakadun da Tinubu ya gabatar

Majalisar dattawa ta amince da naɗin mutum uku na farko da shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya gabatar mata domin tantancewa a matsayin jakadun Najeriya a ƙasashen waje.

Sabbin jakadun da majalisar ta amince da naɗin nasu su ne Aminu Muhammad Dalhatu daga Jihar Jigawa, Lateef Kayode Kolawole Are daga Jihar Ogun, da kuma Emmanuel Ayodele Oke, CFR, daga Jihar Oyo.

Majalisar ta amince da naɗin ne bayan la’akari da rahoton kwamitin majalisar dattawa kan harkokin waje, wanda ya gudanar da tantancewar waɗanda aka gabatar a makon da ya gabata.

Sai dai har yanzu akwai ragowar wasu 64 da shugaba Tinubu ya aike wa Majalisar Dattawa, waɗanda aka tantance amma ba a kai ga tabbatar da naɗin nasu ba.

Shugaba Tinubu ya tura sunayen waɗannan jakadu uku ne a ranar 26 ga Nuwamba.

Wannan shine jerin sunaye na farko na jakadu da Shugaban ƙasa ya miƙa wa Majalisar Dattawa tun bayan hawansa mulki a ranar 29 ga Mayu, 2023.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com