An samu gagarumar raguwar matalar tsaro a Zamfara – Sojoji

Babban kwamandan runduna da ɗaya ta sojin Najeriya da ke Gusau, Birgediya Janar Mustapha Jimoh, ya ce ayyukan ƴanbindiga da ƴanta’adda a jihar Zamfara sun yi matuƙar raguwa.

Yayin da yake jawabi ga manema labarai a wani taro na musamman da rundunar ta shirya a birnin Gusau, Janar Jimoh ya ce hare-haren soji a jihar ƙarƙashin rundunar Fansan Yamma sun yi matuƙar inganta tsaro da zaman lafiya a jihar, kamar yadda gidan talbijin na Channels ya ruwaito.

Janar Jimo ya ƙara da cewa matakin ya sa a yanzu mazauna jihar da matafiya za su yi tafiye-tafiyensu cikin kwanciyar hankali ba tare da fargabar hare-haren ƴanbindiga ba.

“Za ku iya zama shaida a yanzu za ku iya yin tafiya daga Funtua zuwa Gusau, ko Gusau zuwa Sokoto ba tare da wata fargaba ba, don haka za mu iya cewa an samu gagarumar raguwar matsalar tsaro a jihar Zamfara”, in ji shi.

Kwamandan rundunar sojin ya ce rundunarsa za ta ci gaba da ƙoƙari wajen kakkaɓe ragowar ayyukan ƴanbindigar ba a Zamfara kawai ba, har ma da sauran jihohin arewa maso yammacin Najeriya da ma ƙasar baki ɗaya.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com