Sojojin sun gano makeken kabarin ƴan Boko Haram a yankin Timbuktu

Rundunar sojin Najeriya ta bayyana cewa sojojin haɗin gwiwarta na Operation Haɗin kai da JTF sun gano wani makeken kabarin wasu mayaƙan Boko Haram a yankin Timbuktu, wanda aka ƙiyasta yana ɗauke da gawarwaki guda 20 da aka kashe.

Sanarwar rundunar ta ce wannan kabarin an gano shi ne yayin da sojoji ke ci gaba da ayyukan samame da ragargazar ‘yanbindiga a yankin, musamman a wani tashar jiragen ruwa da ke kilomita 6 arewa da Chilaria.

A yayin samamen, sojojin sun gamu da motoci biyu masu ɗauke da abubuwan fashewa.

Duk da cewa sun samu nasarar kawar da ɗaya daga cikin motocin, ɗayan motar ta fashe, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar wasu daga cikin sojojin da kuma raunata wasu.

An gaggauta ɗaukar waɗanda suka ji rauni zuwa asibiti domin samun kulawa, yayin da rundunar ke ci gaba da ayyukanta na tabbatar da tsaro a yankin.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com