Home Labarai Farfesa Abdullahi Pakistan ya bayyana dalilinsa na ajiye shugaban Hukumar NAHCON

Farfesa Abdullahi Pakistan ya bayyana dalilinsa na ajiye shugaban Hukumar NAHCON

Tsoho shugaban hukumar kula da aikin Hajji ta Ƙasa (NAHCON), Farfesa Sheikh Abdullah Saleh Usman, ya bayyana dalilan da suka sanya shi ya ajiye aiki a matsayin shugaban hukumar, wanda ya fara aiki daga ranar Litinin, 9 ga Fabrairu, 2026.

A wata sanarwa da ya fitar wadda da ya sanyawa hannu da kansa, Farfesa Abdullahi Saleh Usman ya bayyana cewa murabus ɗin nasa ya biyo bayan dalilai na kansa, bayan yin dogon tunani, addu’a da shawarwari da iyalansa.

Ya jaddada cewa matakin nasa ba shi da alaƙa da wata matsala ko rashin jituwa da Gwamnatin Tarayya ko hukumar NAHCON.

Tsohon shugaban NAHCON ya tabbatar da cewa ya miƙa takardar murabus ɗinsa a rubuce ga Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, kamar yadda Sashe na 3(6) na Dokar Kafa Hukumar NAHCON ta shekarar 2006 ya tanada.

Farfesa Abdullahi Saleh Usman ya nuna godiya ga Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu bisa amincewa da damar da ya ba shi na yi wa ƙasa da al’ummar Musulmi hidima, tare da yabawa Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima kan shawarwari da goyon bayan da ya ba shi.

Haka kuma, ya miƙa godiya ga Mambobin Kwamitin Gudanarwa, ma’aikata da shugabannin sassan hukumar, yana mai yaba jajircewa da sadaukarwarsu wajen inganta aikin Hajjin Najeriya.

Ya kuma gode wa Hukumomin Jin Daɗin Alhazai na Jihohi, Kamfanonin Hajji, Kamfanonin Jiragen Sama da hukumomin Saudiyya bisa kyakkyawan haɗin gwiwa.

A ƙarshe, Farfesa Abdullahi Saleh Usman ya yi addu’ar Allah Ya karɓi ayyukan da aka gudanar, Ya jagoranci sabon shugabancin NAHCON, tare da roƙon Allah ya sa alhazan Najeriya su yi Hajji karɓaɓɓe (Hajj Mabrur)

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Dangote ya ƙara farashin man feturHukumar Jin dadin alhazan Kano ta sanar da ranar fara jigilar maniyatantaYadda Lakurawa suka kashe masallata a KebbiDSS ta kama jagoran ISWAP da ake nema ruwa a jallo a EdoBa mu taɓa goyon bayan musguna wa Kristoci ba - Gwamnatin NajeriyaGobara ta tashi a babban kasuwar Fika da ke jihar YobeWaye Tunji Disu: Sabon Babban Sifeton 'Yansandan NajeriyaNijar ta amince da kundin ayyukan AES na shekara ta biyuAtiku ya zargi gwamnatin Tinubu da yi wa dimokuraɗiyya zagon ƙasaGwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige FubaraMasu haƙar ma’adinai 33 sun mutu sakamakon gubar sinadarin carbon a FilatoSojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta'addanci
X whatsapp