Home Labarai Rundunar sojin Najeriya ta tura dakaru na musamman zuwa Filato don daƙile...

Rundunar sojin Najeriya ta tura dakaru na musamman zuwa Filato don daƙile ƴanbindiga

Rundunar sojin ƙasa ta Najeriya ta sanar da tura dakaru na musamman zuwa jihar Filato domin daƙile ayyukan ’yan bindiga da kuma fuskantar sabon ɓarkewar hare-haren rashin tsaro a jihar.

Matakin ya biyo bayan amincewar da Babban hafsan sojin ƙasa, Laftanar Janar Waidi Shaibu, ya bayar na tura Rundunar ta musamman zuwa yankin.

Sanarwar da rundunar ta fitar ta ce, “dakarun, waɗanda tuni suka isa Jihar Filato, za su gudanar da ayyuka masu tsauri da farmaki kai tsaye domin murkushe ’yan bindiga da sauran masu aikata laifuka.”

Rahotanni sun nuna cewa rundunar na da horo na musamman da kayan aiki na zamani da ake sa ran za su taimaka wajen sauya yanayin tsaro a jihar.

Yayin karɓar dakarun a hedikwatar Rundunar Soji ta 3 Division, babban kwamandan rundunar, Manjo Janar Folusho Oyinlola ya yaba da jagorancin gaggawa da Shugaban Sojin Kasa ya nuna wajen samar da muhimman kayan yaƙi da sauran kayayyakin aiki da za su ba dakarun damar aiwatar da aikinsu yadda ya kamata.

Ya bayyana cewa wannan goyon baya zai taimaka matuƙa wajen cimma nasarar ayyukan tsaro a jihar.

Haka kuma, ya yi kira ga al’ummar Jihar Filato da kada su firgita idan suka ga yawan motsin sojoji da manyan kayan aikin soja.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Dangote ya ƙara farashin man feturHukumar Jin dadin alhazan Kano ta sanar da ranar fara jigilar maniyatantaYadda Lakurawa suka kashe masallata a KebbiDSS ta kama jagoran ISWAP da ake nema ruwa a jallo a EdoBa mu taɓa goyon bayan musguna wa Kristoci ba - Gwamnatin NajeriyaGobara ta tashi a babban kasuwar Fika da ke jihar YobeWaye Tunji Disu: Sabon Babban Sifeton 'Yansandan NajeriyaNijar ta amince da kundin ayyukan AES na shekara ta biyuAtiku ya zargi gwamnatin Tinubu da yi wa dimokuraɗiyya zagon ƙasaGwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige FubaraMasu haƙar ma’adinai 33 sun mutu sakamakon gubar sinadarin carbon a FilatoSojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta'addanci
X whatsapp