Home Labarai Hisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a Kano

Hisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a Kano

Hukumar Hisbah a jihar Kano ta ce jami’anta sun kama wasu mutum tara Musulmai a jiya Laraba a take ranar farko ta azumin watan Ramadan saboda an gan su suna cin abinci da tsakar rana.

Jihar Kano na da yawan Musulmai, inda tsarin shari’ar Musulunci ke aiki tare da dokokin ƙasa na yau da kullum.

A kowane Ramadan, Hisbah na bincika wuraren sayar da abinci da kasuwanni domin tabbatar da cewa Musulmai na bin dokokin azumi.

A wasu wurare, wurarern cin abinci na ci gaba da aiki musamman a yankunan da Kiristoci da dama ke zaune.

Ga Musulmai masu azumi, cin abinci daga fitowar rana zuwa faduwar rana haramun ne.

Yin azumi na daga cikin ginshikan Musulunci guda biyar da ke kafa yadda Musulmai ke gudanar da rayuwarsu.

Mujahid Aminudeen, mataimakin kwamandan Hisbah, ya shaida wa BBC cewa daga cikin wadanda aka kama akwai mata biyu da maza bakwai.

Ya ce: “Mun kama su kuma suna tare da mu inda za mu koya musu muhimmancin azumi, yadda za su yi salla da karanta Al-Qur’ani, kuma su zama Musulmai nagari.”

Ba a bayyana lokacin da Hisbah za ta saki wadanda aka kama ba.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Dangote ya ƙara farashin man feturHukumar Jin dadin alhazan Kano ta sanar da ranar fara jigilar maniyatantaYadda Lakurawa suka kashe masallata a KebbiDSS ta kama jagoran ISWAP da ake nema ruwa a jallo a EdoBa mu taɓa goyon bayan musguna wa Kristoci ba - Gwamnatin NajeriyaGobara ta tashi a babban kasuwar Fika da ke jihar YobeWaye Tunji Disu: Sabon Babban Sifeton 'Yansandan NajeriyaNijar ta amince da kundin ayyukan AES na shekara ta biyuAtiku ya zargi gwamnatin Tinubu da yi wa dimokuraɗiyya zagon ƙasaGwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige FubaraMasu haƙar ma’adinai 33 sun mutu sakamakon gubar sinadarin carbon a FilatoSojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta'addanci
X whatsapp