Majalisar Dokokin Jihar Rivers ta dakatar da shirin saukewa daga mukami Gwamna Siminalayi Fubara da Mataimakinsa, Ngozi Odu, bayan tsoma bakin Shugaban Kasa, Bola Tinubu.
Majalisar ta ɗauki matakin dakatar da shirin tsige gwamnan ne a ranar Alhamis, yayin zaman da aka ci gaba da gudanarwa a birnin Port Harcourt, babban birnin jihar.
Tun daga farkon wannan shekara ne wasu ‘yan majalisar suka fara magana kan yiwuwar tsige gwamnan saboda zarge-zarge kan yadda wasu ayyukan gwamnati ke tafiya da kuma rikice-rikicen siyasa a jihar.











