Home Labarai Sojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da...

Sojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a Adamawa

Dakarun sojojin Najeriya karkashin Operation HADIN KAI sun sami wannan nasara ne sakamakon wani sumame da suka kai domin dakile ayyukan mayaƙan Boko Haram a yankin Arewa maso gabashin Ƙasar.

A sumamen sun sami nasarar hallaka mayakan ƙungiyar Boko Haram biyu ciki harda kwamandanta Abdullahi Mafa, wanda ya jima yana jagorantar hare- hare a yankin Madagali

Wata majiyar tsaro ta shaida cewa da misalin karfe 5:30am ranar Alhamis sojojin haɗin gwiwa da Jami’an bijilanti da mafarauta suka aikawa mabiyan ƴan ta’addan kusa da kogin Visil a karamar hukumar Mafarki dake jihar.

Haka kuma dakarun sun tasamma tashar mota ta Madagali da misalin karfe 6:30 inda suka kama wani mutum mai kimanin shekaru 64 mai suna Dauda Usman wanda ke matsayin mai sayarwa da ƴan Boko Haram jirgi maras matuka wai Done da wasu kayayyakin amfanin yau da kullum.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Dangote ya ƙara farashin man feturHukumar Jin dadin alhazan Kano ta sanar da ranar fara jigilar maniyatantaYadda Lakurawa suka kashe masallata a KebbiDSS ta kama jagoran ISWAP da ake nema ruwa a jallo a EdoBa mu taɓa goyon bayan musguna wa Kristoci ba - Gwamnatin NajeriyaGobara ta tashi a babban kasuwar Fika da ke jihar YobeWaye Tunji Disu: Sabon Babban Sifeton 'Yansandan NajeriyaNijar ta amince da kundin ayyukan AES na shekara ta biyuAtiku ya zargi gwamnatin Tinubu da yi wa dimokuraɗiyya zagon ƙasaGwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige FubaraMasu haƙar ma’adinai 33 sun mutu sakamakon gubar sinadarin carbon a FilatoSojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta'addanci
X whatsapp