Home Labarai Nijar ta amince da kundin ayyukan AES na shekara ta biyu

Nijar ta amince da kundin ayyukan AES na shekara ta biyu

Jamhuriyar Nijar ta amince da kundin ayyukan Ƙungiyar Kasashen Sahel (AES) na shekara ta biyu wadda ta haɗa da Mali da Burkina Faso, kafin taron ministoci da za a gudanar a Ouagadougou daga 24 zuwa 26 ga watan Fabrairu, kamar yadda jaridar gwamnati ta ANP ta ruwaito a ranar 21 ga Fabrairu.

Firaminista Ali Mahamane Lamine Zeine ya gana da ministoci da mambobin kwamitin ƙasa na AES a ranar 21 ga Fabrairu domin daidaita matsayi kafin taron yankin.

Mataimakiyar Shugabar kwamitin, Bayard Mariama Gamatie, ta ce Burkina Faso ta raba wani kundin aiki, wanda Nijar ta gyara bisa ginshiƙai uku da suka haɗa da tsaro da diflomasiyya, ci gaban ƙasa, da tsaro da kare iyaka.

“An amince da kundin gaba ɗaya, dangane da shawarwarin gyare-gyaren Nijar,” in ji Gamatie.

Rahoton ya nuna cewa ministocin Nijar sun duba kundin sun kuma yi gyare-gyare da sake fasalta wasu abubuwa, sannan sun bayar da shawarwari don taron ƙwararru da zai biyo baya.

An kafa AES a shekarar 2023, bayan da ƙasashen uku suka janye daga Ƙungiyar ECOWAS, domin tsara manufofi na tsaro da diflomasiyya, da ci gaban ƙasa tsakanin ƙasashen Sahel.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Nijar ta amince da kundin ayyukan AES na shekara ta biyuAtiku ya zargi gwamnatin Tinubu da yi wa dimokuraɗiyya zagon ƙasaGwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige FubaraMasu haƙar ma’adinai 33 sun mutu sakamakon gubar sinadarin carbon a FilatoSojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta'addanciGwamnatin Najeriya da gwamnonin APC sun bai wa ƴan kasuwar Singer tallafin biliyan 8Kwankwasiyya ta yi martani kan matakin majalisar Amurka na hukunta KwankwasoSojojin Najeriya sun daƙile hare-haren mayaƙan ISWAP a BornoFarfesa Abdullahi Pakistan ya bayyana dalilinsa na ajiye shugaban Hukumar NAHCONMajalisar Najeriya ta kafa kwamitin nazari kan gyaran dokar zaɓeRundunar sojin Najeriya ta tura dakaru na musamman zuwa Filato don daƙile ƴanbindigaMajalisar Dinkin Duniya da Turkiya sun yi Alla-wadai da harin da aka kai Kwara
X whatsapp