Shugaban Rundunar Sojin Kasa ta Najeriya (COAS), Laftanar Janar Waidi Shaibu, ya bukaci jami’ai da dakarun sojin kasar su mutunta hakkin bil’adama tare da ba da fifiko ga kare rayukan fararen hula a dukkan ayyukan soja.
Ya bayyana haka ne yayin da yake batar da Makala mai take (Command Philosophy) ga dakarun da suka halarci kwas a Kwalejin koyon dabarun yaki dake birnin tarayya Abuja a ranar Talata
Read Also:
Shaibu ya jaddada cewa bin dokokin ƙasa da ƙasa da suka shafi yaƙi, ciki har da dokokin jin ƙai na duniya (International Humanitarian Law) da kuma ƙa’idojin aiki na soja wato (Rules of Engagement), ba wai kawai wajibi ne a doka kadai ba, har ma yana da muhimmanci wajen samun nasara a fagen daga.
A cewarsa, wannan tsari zai taimaka wa jami’ai su yi aiki yadda ya kamata a cikin yanayin tsaro mai rikitarwa da ke sauyawa a kullum.
Shaibu, ya bayyana cewa sabbin dabarun aikin sojin Najeriya na ci gaba da inganta bisa yadda rundunar ke tinkarar barazanar tsaro na zamani, musamman irin na yaƙin ‘yan tada ƙayar baya, wanda haɗa kai da fararen hula ke da matuƙar muhimmanci wajen samun nasara.
A nasa jawabin, kwamandan Kwalejin koyon dabarun yaki, Manjo Janar Umar Alkali, ya yabawa COAS bisa ci gaba da bai wa makarantar goyon baya, yana mai cewa jawabin ya ƙara wa mahalarta da makarantar ilimi da kwarewa sosai.












