Dakarun Rundunar ‘Yan sandan Jihar Kano dake Arewacin Nijeriya ta sami nasarar kame wasu matasa da take zargi da ayyukan fashi da makami a gidan wani dan Indiya dake jihar,
Wannan na kunshe ta cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun kakakin rundunar SP Abdullahi Haruna Kiyawa ANIPR, wadda kaka raba ga manema labarai, sanarwa tace dakarun hukumar na Kan Kace Kwabo Wato (Operation Puff Adder), bisa jagorancin baturen ‘Yan sanda dake lura da shiyyar sharada a karamar hukumar Birnin da kewaye na jihar, sun sami wani bayanin sirri, kuma basuyi kasa a gwuiwa ba suka shiga aiki gadangadan, nan suka sami nasarar kame guda cikin wadanda ake zargin a cikin wani babur din Adaidaita Sahu a kofar gidan Dan Indiyan.
Kiyawa yace ko da matukin babur Din mai suna Alh. Musa Mai kimanin shekara 45 dan unguwar Tudun Rubudi ya hangi dakarun ‘yan sanda yayi yunkurin ranta a na kare, said ai dakarun Yan sanda sun harbi tayar Babur din nasa.
Read Also:
Matukin babur din da wani matashi Onyekachi Jude mai kimanin shekaru 19 dan Unguwar Rinji, a jihar kano, sun shiga hannun dakarun ‘yan sandan, sai dai Harbin da dakarun ‘yan Sanda sukayi tun da fari yaja hankalin ‘yan fashin dake cikin Gidan Dan Indiya nan sukayi kokarin guduwa, a kokarin nasu na guduwa dakarun ‘yan sandan sun sami nasarar kamei i). Moses Jude, dan shekara 23, dan unguwar Rinji,
da Sunday Titus, mai kimanin shekaru 20 dan unguwar Zoo Road Kano
sai Kyunle Bhago, mai kimanin shekaru 22 a duniya dan Sabuwar Gandu duk a jihar ta Kano.
Sanarwar tace tun a binciken farko da aka gudanar kan wadanda ake zargin sun amsa cewa Musa ya zauna a gidan a baya, inda suka hada baki da wasu mutane uku kuma suka je gidan dan kasar Indiya a lokuta da dama, sai yayin da ‘yan sandan suka yi musu kofar rago guda cikin su ya tsere da wayar salula ta kimanin Naira Dubu 50 da kudi kimanin Dala, amma an sami damar kwato kayayyaki a hannun barayin da suka hadar da wayar kirar Honor, wuka mai kaifin, Takunkumin badda bami, da Na’urar shiga Yanar gizo ta Modem, sai kuma kudin kasar Indiya da yaka Rufi 550 da kuma wata jakar takardu.
Kakakin yace tuni Kwamshinan Sama’ila Shu’aibu Dikko, fsi ya bada umarnin yin bincika kan wadanda ake zargi inda daga bisani za’a mikasu gaban kuto domin yin abinda ya dace.
SP ABDULLAHI HARUNA KIYAWA, ANIPR,
POLICE PUBLIC RELATIONS OFFICER,
FOR: *COMMISSIONER OF POLICE, KANO STATE COMMAND.*
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1254 days 15 hours 34 minutes 14 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1236 days 17 hours 15 minutes 39 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com