Rundunar ‘Yan Sandan ihar Zamfara Na Samun Nasara A Yakin Da Take Da ‘Yan Ta’addan

Rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara ta ce masu kwarmatawa ‘yan ta’adda bayanan sirri sune matsalar rashin tsaron jihar kuma a sannu hukumar na samun nasarar kakkabe su.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar SP Muhammad Shehu ne ya bayyana hakan yayin da yake ganawa da wakilin jaridar PRNigeria Hausa ta wayar tarho a safiyar juma’a.

kakakin rundunar ‘yan sandan Jihar SP Muhammad Shehu ya bayyana cewa hukumar na samun gagarumar nasara a yakin da suke da ta’addanci a jihar.

“Akwai wadanda ake kira masu kwarmata bayanan sirri ga ‘yan bindiga, suna daga cikin masu bamu matsala”.

“Amma bisa hadin gwuiwar jami’an rundunar yan sanda da Al’ummar gari, wadanda ke son taimakawa  muna Aiki da su ka’in da na’in wajen zakulo  wadannan bata garin mutane domin kama su a gurfanar da su gaban kotu”

“Irin wadannan mutane mun kama su da yawa mun kuma gurfanar da su gaban kotu, yanzu haka an kai su gidan gyaran hali.

Daga bisani ya bayyana cewa a wajen hukumar ‘yan sanda masu bayyana wa ‘yan ta’adda bayanan sirri, sun fi ‘yan bindigar laifi kasancewa suke bayyana musu inda ya kamata su kai hari da yadda zasu yi garkuwa da mutane.

“suke bayyanawa wadannan bata gari rahoto akan wanda ya kamata a sace, inda ya kamata su kai hari wurin da ya kamata a ka hari kaga kuwa sune ya kamata a kawar da su daga cikin Al’umma”. In Ji shi.

Wannan dai na zuwa ne  bayan samun labarin dake cewa ‘yan bindiagr da suka yi garkuwa da masu sana’ar sayar da waya a kan hanyar su ta komawa jihar Zamfara dake arewacin Nijeriya.

Duk da cewa labarin bai baina ko an biya kudin fansa ba ko akasin haka, ko da yake an rawaito cewa sai da ‘yan bindigar suka musu dukan kawo wuka kafin sakin su.

jihar Zamfara dai na guda cikin jihohin dake Arewa maso Yammacin kasar dake fama da matsalar rashin tsaro.

 

Kidnapped School Children

Yauri FGC Students, Kebbi
1254 days 14 hours 47 minutes 48 seconds,

Baptist School Students, Kaduna
1236 days 16 hours 29 minutes 13 seconds

Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Spent 88 days from May 30, 2021 - August 26, 2021


Report By: PRNigeria.com

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com