Ministan kwadago da samar da aikin yi na Najeriya, Chris Ngige ya damka takardar shaida ga kungiyar ma’aikatan koyarwa a jami’o’in Najeriya, wadda kungiya ce ta malaman jami’o’in tarayya da na jihohi.
Kungiyar mai suna CONUA a takaice ana ganin kai tsaye za ta kasance kishiya ga babbar kungiyar malaman jami’o’in Najeriya wato ASUU.
Wani jami’in gwamnatin Najeriya ya wallafa cewa an kafa kungiyar CONUA ne a shekara ta 2018 a jami’ar jihar Osun.
Read Also:
Kungiyar ASUU da gwamnatin Najeriya na kai ruwa rana saboda yajin aikin sai-baba-ta-gani da malaman jami’o’in suka shiga tsawon wata takwas ke nan yanzu, suna neman sai lallai gwamnati ta biya musu bukatunsu.
Duk da wani kokari da ban-baki da tattaunawa daga gwamnati sun kasa shawo kan kungiyar malaman kungiyar ASUU dakatar da yajin aiki.
Baya ga kungiyar CONUA, ministan kwadagon ya kuma amince da kungiyar likitoci masu koyarwa ta kasa (NAMDA)
an dai sami tirka-tirka tsakanin kungiyar malaman jami’ar ta ASUU da Gwamnatin tarayya Nijeriya, duk da cewa sun zauna zaman sulhu a tsakani amma ana kallon hakan yaci tura, ko da yake ana kallon samar da wannan kungiyar matsayin wani matashi na rage karfin kungiyar malaman ta ASUU.
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1254 days 21 hours 18 minutes 43 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1236 days 23 hours 8 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com