Gwamnatin jihar Zamfara ta amince ta aiwatar da mafi karancin albashin naira dubu 30 ga ma’aikatan jihar.
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwar da babban daraktan yada labarai na ofishin mataimakin gwamna, Babangida Umar, ya fitar ranar Laraba a Gusau, babban birnin jihar, sanarwar tace mataimakin gwamna, Sanata Hassan Nasiha, ya sanar da hakan ne yayin karbar takardar yarjejeniyar da gwamnati ta kulla da ma’aikatan.
Mataimakin gwamnan ya nuna jin dadinsa game da yadda kungiyar kwadago ta nuna girma da fahimta yayin yarjejeniya da ma’aikatan gwamnati.
Read Also:
Fahimtarsu ta sa aka yanke shawarar aiwatar da mafi karancin albashi na N30,000 a watan Nuwamba.
“Halin da ake ciki na tabarbarewar tattalin arziki da kalubalen tsaro na cikin abubuwan da gwamnati ta yi la’akari da su kafin ta amince da aiwatar da sabon albashin,” in ji shi.
Ya kuma yaba wa kwamitin da Ambasada Bashir Yuguda ya jagoranta da ya wakilci gwamnati wajen cimma matsaya da kungiyoyin kwadago cikin lumana.
(NAN)
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1254 days 23 hours 12 minutes 7 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1237 days 53 minutes 32 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com