Ma’aikatan Jinya na Gaggawa Sun yi Alkawarin Bada, Magunguna Kyauta ga Membobin NURTW a Kwara

Daga Fatima Mohammed-Lawal

Kungiyar ma’aikatan jinya ta gaggawa wato Emergency Nurses Assoiation of Nigeria (ENAN) reshen jihar Kwara ta yi alkwarin duba lafiya gami da bada magunguna kyauta ga mambobin kungiyar sufuri ta (NURTW), ta jihar.

Kamfanin dillanci labarai na Nijeriya NAN ya ruwaito cewa wannan na wani bangare na bikin makon ma’aikatan gaggawa na duniya na shekarar 2022, wanda aka yiwa take “ standing strong”

Ayyukan kiwon lafiya sun hadar da duba marasa lafiya kyauta gami da bada magani kyauta, sai kuma gwajin shan miyagun kwayoyi, dakuma bada gajin gaggawa ga mambobin kungiyar da hadari ya rutsa dasu.

Da take jawabi a yayin taron bikin shugabar kungiyar Mrs Bashirat Dere, tace an ware ranar ne domin yin murna da irin gudunmawar da ma’aikatan jinyar ke bayarwa ga Al’umma, hadi da bayyana irin kalubalen da suke fuskanta da kuma walwalar su.

Dere ta bayyana bangare likitocin Jinya na gaggawa fannin ne na kwararru a cikin likitocin jinya, wanda ke mayar da hankali a bangare lura da marasa lafiya da ke bukatar kulawar ta musamman domin tserartar dasu daga mutuwa.

A cewar ta, ma’aikatan jinya na gaggawa suna lura da marasa lafiya da ke fama da rauni ko kuma yanayin rashin  lafiya mai tsananni wadda ke bukatar kulawar gaggawa.

Masaniyar ta tabbatar da cewa tun da wadannan kwararrun suna aiki a cikin yanayi na rikici, dole ne su iya hanzarta gano hanya mafi kyau don ura da marasa lafiya da kuma rage musu zugi.

Ta kuma bukaci mahukunta a kowanne mataki dasu lura da walwala da jin dadin mambobin wannan kungiya.

Da yake jawabi Babban Daraktan asibitin koyarwa na jami’ar Ilorin (UITH), Farfesa Abdullahi Dasilva, yay aba da kwazon aiki da sadaukarwar ma’aikatan jinyar na gaggawa wajen ceto rayukan Al’umma.

Ya kuma bukace su dasu tsaya kai da fata wajen gudanar da ayyukan su, wajen  ceto rayukan Al’umma.

Dasilva ya kuma yi alkawarin cewa cibiyar lura da lafiya ta manyan makarantu za ta ci gaba da talafawa mambobin ta hanyar horarwa da sake horardama’aikatan ta.

 

Kidnapped School Children

Yauri FGC Students, Kebbi
1190 days 11 hours 58 minutes 17 seconds,

Baptist School Students, Kaduna
1172 days 13 hours 39 minutes 42 seconds

Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Spent 88 days from May 30, 2021 - August 26, 2021


Report By: PRNigeria.com

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com