Hukumar zaɓen Najeriya ta bayyana sakamakon zaɓen gwamnan jihar Kebbi a matsayin wanda bai kammala ba.
Babban jami’in tattara sakamakon zaɓen jihar Farfesa Yusuf Sa’idu na jami’ar Usman Danfodio da ke Sokoto ne ya bayyana haka a cibiyar karɓar sakamakon zaɓen da ke Birnin Kebbi.
Ya ce an samu yawan ƙuri’u da aka soke a rumfunan zaɓe da dama a faɗin ƙananan hukumomi 20, daga cikin 21 na jihar.
Fafatawar dai ta fi zafi ne tsakanin manyan jam’iyyun APC mai mulkin jihar da kuma jam’iyyar PDP mai hamayya.
Read Also:
Farfesa Sa’idu ya ce adadin katin zaɓen da aka karɓa a wuraren da aka soke zaɓen ya kai 91,829.
“Sakamakon da muka tattara yanzu ya nuna cewa jam’iyyar APC na da yawan ƙuri’u 388,258, yayin da PDP ke da ƙuri’a 342,980. Dan haka idan muka duba bambancin da ke tsakaninsu shi ne ƙuri’a 45,278,” in ji Farfesa Sa’idu.
Dan haka a cewarsa ba abin da ya kamata a yi sai komawa sashe 51 ƙaramin sashen biyu da na uku, na dokar zaɓe ta 2022.
Wanda ya tanadi cewa idan adadin ƙuri’un da aka soke ya zarta adadin tazarar ƙuri’un da ke tsakanin ‘yan takara to dole sai an sake zaɓe a wuraren da aka soke zaɓukan.
PRNigeria Hausa
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1239 days 16 hours 50 minutes 37 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1221 days 18 hours 32 minutes 2 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com