Wani bincike da jaridar PRNigeria ta gudanar ya tabbatar da cewa Dan takarar jam’iyyar Labour Party na mazabar Surulere a zauren majalisar jihar Legas, Olumide Oworu, bai ji ciwo ba a zaben daya gabata ranar asabar.
Idan za’a iya tunawa an ta yada wani hoto a shafin Facebook na Oworu da yake nuna yadda yake zubar da jini a yanar gizo yana mai bayyana cewa an kai masa hari shi da tawagar sa abinda ya haddasa masa jikka a yayin zaben.
Haka kuma an ta yada hotunan a kafafen sada zumunta na zamani ciki har da shafin WhatsApp
amma PRNigeria tayi amfani da manhajar binciken hoto ta “reverse image search” kan hoton na Oworu.
Read Also:
Sakamakon ya nuna cewa Oworu da kan ne y afara wallafa hoton da jini a jikin sa a shafukan sada zumunta tun a watan Oktoban shekarar 2022, mai taken “Alagbado John Wick #OntheEdge,”
Haka kuma wani sakamako ya nuna makamancin hoton na dankarar majalisar jihar karkashin inuwar jam’iyyar LP a shafin Instagram na fitacciyar mai yin kwalliya, Carina Ojoko.
PRNigeria ta gano cewa wannan hoton an samo shi ne a cikin wani Shirin wasan kwakwayo mai suna “ On the Edge” bashi da hadi da harin kwanannan da aka ce an kaiwai dan takarar.
Dan haka dangane da binciken da PRNigeria ta gunadar, wannan hoton Olumide Oworu ya fito ne daga wani shiri na “On the Edge,” ba a lokacin harin aka samo shi ba.
Wannan ya sanya PRNigeria ta bayyana labarin matsayin na karlya da kanzon kurege.
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1239 days 14 hours 55 minutes 3 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1221 days 16 hours 36 minutes 28 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com