Mataimakin gwamnan jihar Kano kuma ‘dan takarar Jam’iyyar APC a zaben da aka yi ranar Asabar, Dakta Nasir Yusuf Gawuna ya ce, hukumar zabe ta yi kuskure wajen bayyana Abba Kabir Yusuf a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar sakamakon soke zaben wasu mazabun da aka yi.
Read Also:
- An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa’adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDP
- AIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da Zamfara
- Sojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta’addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a Sokoto
Mataimakin gwamnan ya ce lura da yadda hukumar zaben ta bayyana zaben ‘yan majalisun jihar Kano 16 a matsayin wadanda ba su kammala ba, wato ‘inconclusive’ ya dace ace ta dauki wannan mataki a zaben kujerar gwamnan.
Gawuna ya ce suna da yakinin cewar Allah ke bada mulki ga wanda ya so a lokacin da yake so, saboda haka za su bi matakan da suka dace ta fannin shari’a domin neman hakkinsu.
Mataimakin gwamnan ya jinjina wa mutanen Kano akan irin goyan bayan da suka ba shi, yayin da ya bukaci kwantar da hankali da kuma kauce wa daukar doka a hannu.
Shi ma a nasa jawabi, shugaban masu rinjaye a majalisar wakilai ta kasa Hon. Alhassan Ado Doguwa ya ce dokar zabe ta yi tanadin cewar, idan an soke zabe a wasu mazabun da kan iya shafar kammalalen sakamakon baki daya, ya zama wajibi a koma domin sake gudanar da zabe a wadannan wurare kafin gabatar da kammalallen sakamako.
Ita dai hukumar zabe ta bayyana Abba Kabir Yusuf na jam’iyyar NNPP a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan da kuri’u sama da miliyan guda.












