Hukumomin dake karkashin ma’aikatar cikin gida, wanda suka hadar da *NIS, NSCDC, FFS da NCS* sun koka kan yadda maganar karin albashinsu taki ci taki cinyewa, inda suke korafin cewa rayuwar tana musu wahala musamman duba da yadda sauran jami’ai yan uwansu, kamar Police, Custom, DSS da EFCC, sukayi musu fintinkau a harkar albashi, jamian sunce an dade ana ja musu rai akan karin, yayin da ko yaushe ake nuna musu yau ko gobe, a haka suka shafe tsawon shekaru biyu (2) da wani abu suna jiran gawon shanu, a baya-bayannan ne, daf da karewar shekarar 2022 akayi zama da hukumar kudi da tsare-tsare (ministry of finance) akan yadda zaa daidaita albashin nasu da hukumar yansanda, har aka fitar da jawabai kan cewa, zaa biyasu sabon tsarin albashin da yake dauke da karin kaso 40% na albashin nasu a karshen December, ta 2022, sannan a watan January kuma zaa biyasu arreas na wata 3, amma dai har yanzu shiru sukeji kamar an shuka dusa, bayan haka yanzu akayi maganar karin albashi ga ma’aikatan gwamnatin tarayya, a karshen watan Aprilu, se gashi shima Karin ya bayyana babu wadannan jami’ai.
#Shin lefine ka zama a karkashin ita wannan ministry
#shin lefine kazama dan kasa na gari
#ko aikin nasune bashi da muhimmanci ga alumma ko ga gwamnatin tarayya.
Akarshe muna rokon gwamnati da ta duba alamarin wadannan jami’ai masu yi mata hidima babu dare babu rana.
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1254 days 15 hours 2 minutes 4 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1236 days 16 hours 43 minutes 29 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com