Cibiyar binciken kwakwafi ta Wole Soyika ta yabawa da kwazon jaridun PRNigeria da Economic confidential.
Cibiyar binciken kwakwafi ta Wole Soyinka, WSCIJ ta bayyana gamsuwarta bisa kokarin Jaridun PRNigeria da Economic Confidential suka nuna a wani hadin gwiwa da tayi da su domin cigaba.
Dukkan jaridun na PRNigeria da Economic Confidential, wani yanki ne dake karkashin inuwar kamfanin Image Merchants Promotion (IMPR), na cikin zababben kafafen yada labarai 26 da cibiyar ta WSCIJ zaba bisa tallafin gidauniyar MacArthur.
Read Also:
Babbar daraktan cibiyar Mrs. Motunrayo Alaka, ta bayyana hakan yayin da jagorancin tawagar cibiyar zuwa babban ofishin Jaridar dake Abuja, domin bayyana kokarin jaridun.
Ta yabawa jaridun guda biyu dake karkashin kamfanin na IMPR bisa yadda suke wallafa sahihan labarai masu muhimmancin gaske.
Da yake nasa jawabin babban Editan Jaridun Mal. Yushau Shuaib ya bayyana cewa jaridun sun wallafa Labarin binciken kwakwafi, rahotanni na musamman da ya ja hankalin Mahukunta suka dauki mataki kan wasu lamurran da suka shafi al’ummomin Niger, Zamfara, Kebbi da kuma birnin tarayya Abuja.
PRNigeria hausa
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1254 days 19 hours 38 minutes 54 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1236 days 21 hours 20 minutes 19 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com