Harin rundunar sojin saman Nijeriya yayi sanadiyyar tarwatsa maboyar ‘yan ta’adda masu tayar da kayar baya a dajin Sambisa da ke yankin tafkin chadi tare da hallaka mayakan 12.
Ta cikin wata sanarwa da daraktan yada labarai da bayanai na rundunar sojin saman Nijeriya Air Vice Marshal Edward Gabkwet ya fita mai dauke da kwanan watan 7 ga watan Janairu 2024.
Read Also:
Sanarwar ta ce a kokarin rundunar sojin na kakkabe matsalolin rashin tsaron a yankin arewa maso gabashin kasar, rundunar na cigaba da samun nasara, in da a ranar 5 ga watan janairun wannan shekara rundunar ta sami nasara a Parisu bayan wani bayanan sirri da ta samu na yadda ‘yan ta’adda ke karakaina da makamai da alburusai a yankin.
Parisu wani yanki ne dake kusa da dajin sambisa, wanda ‘yan ta’adda suka taba mamaye shi, sai dai daga bisani sojojin Nijeriya suka, harin da ya yi sanadiyya mutuwar mayakn da dama tare da kwace maboyar ta su.
Haka kuma rahotannin sun bayyana cewa ‘yan ta’adda 12 aka hallaka yayin harin dakarun ta sama, tare da tarwatse maboyar su, harin kuma ya dakile yunkurin ‘yan bindigar na kai hari kan dakarun sojojin.
PRNigeria hausa
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1255 days 16 hours 19 minutes 49 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1237 days 18 hours 1 minute 14 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com