Dakarun sojin saman Najeriya da ke aiki ƙarƙashin rundunar ‘Operation Delta Safe’ sun sami nasarar tarwatsa wuraren tace mai ba bisa ƙa’ida ba da jiragen ruwan dakon kaya maƙare da ɗanyen mai da aka sace a yankin Neja Delta.
wannan na kunshe ta cikin wata sanarwa da daraktan yaɗa labarai na rundunar sojin saman Najeriya, Edward Gabkwet, ya fitar wadda ta ce a yayin wani samame da dakarun suka kai kan cibiyoyin da jiragen ruwan dakon kayan tsakanin 25 da 26 ga watan Maris a wasu yankunan jihar Rivers.
Read Also:
An gano wani jirgin dakon kaya a yankin Bille cike da albarkatun mai da aka tace ba bisa ƙa’ida ba. Kazalika, sojojin a yankin Dariama da Tumakiri, wuraren da suka yi suna kan tace mai ba bisa ƙa’ida ba, sojojin sun gano tukwanen girki abin da ke nuna akwai mutane a wajen. Sun kuma yi musayar wuta tsakaninsu inda kuma suka lalata wuraren da ake tace man ba bisa doka ba.
A cewar sanarwar, sojoji sun ƙona wasu wuraren da aka gano ana tace ɗanyen mai ba bisa ƙa’ida ba inda kuma aka cinna masu wuta.
A baya, sojoji sun lalata wuraren da aka gano a Bille da Dariama. Rundunar sojin saman da wasu hukumomin tsaro, a cewar sanarwar za su ci gaba da ƙara ƙaimi wajen gano ayyukan masu satar ɗanyen ma da ke gudanar da ayyukansu a yankin.
PRNigeria Hausa
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1255 days 3 hours 47 minutes 41 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1237 days 5 hours 29 minutes 6 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com