Gwamnan jahar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya yaba wa hukumomin tsaron jahar, bisa matakan da suka dauka wajen dakile aiyukan Daba da kuma kwacen wayoyin al’umma a sassan birnin jihar.
Gwamna Abba Kabir Yusuf, ya bayyana hakan ne a fadar gwamnatin jahar, yayin gabatar da bikin Hawan Nasara a Ranar juma’a.
A cewar gwamnan sun yi kokari wajen hada Kai da jami’an tsaro domin kare rayukan al’umma da dukiyoyinsu, amma duk da haka sai da wasu marasa kishin jahar Kano, wadanda suka dawo da harkar Daba a cikin kwaryar birnin Kano.
“ Mun San su ba wai ba mu San su ba, sun dawo mana da Daba domin basa son cin gaban jahar Kano, kuma basa son zaman lafiya”
Ya Kara da cewa a cikin watan Ramadan da ya gabata, an samu wasu batagarin matasa da suke rubuta wasika su aikata wa Mutane a masallatai, inda suke zuwa tare da farwa Mutane har su Yan yanke su ta Hanyar Daba mu su wukake, sannan kwace mu su wayoyinsu.
“ Ba bu shakka gwamnatin Kano, a karkashin mu ba zata lamunci wannan ta’addanci da ake ba” Gwamnan Kano”.
Read Also:
Gwamnan jahar Kano Abba Kabir Yusuf, ya godiya wa shugabannin hukumomin tsaron jahar , da suka hada da Kwamishinan Yan sandan jahar CP Muhammed Usaini Gumel, Sojojin Kasa, Sojojin Sama, Hukumar tsaron Farin kaya DSS, hukumar gidan gyaran hali, hukumar kwastam da kuma ta shige da fice da dai sauransu.
Ya ce sun matukar kokarin domin dakile ta’addancin da aka shigo da shi , inda suka bi gida-gida wajen Kano dukkan Wanda aka ji labarin yana aikata ta’addanci , kuma aka gurfanar da su a gaban kotu.
Haka zalika gwamnan ya yi Kira ga mai martaba sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero, da su fito tare da hakimansa wajen bayar da gudunmawa don dakile wannan yanayi na ta’addanci.
” bayan an Kai su kotu mutane marasa kishin su suka je kotu, har suka bayar da kudi suka fito da wadanda aka Kama, a saboda haka gwamnatin Kano tana Allah wadai da wannan Abu, kuma su Masu yin hakan ko su Dakata su daina ko kuma gwamnati ta dira akansu” A.K.Y.”.
Ya Kara da cewa gwamnatin jahar Kano tare da hukumomin tsaro da Sarakuna za su Ci gaba da hada Kai, don tabbatar da cewar an ceto al’umma daga halin rashin tabbas da dardar.
” saboda haka mun dau matakai da za mu tabbatar da cewa wannan ta’addanci ya Kau cikin ikon Allah” Abba Kabir “.
Gwamnan ya ce a ko a watannin baya, da fadan Daba ya yi kamari a birnin Kano, sun janyo matasan 222 da suka tuba daga aikata laifuka har gwamnatin kanon, ta ba su sana’o’in dogaro da Kai.
Da yake nasa jawabin mai martaba sarkin Kano, Alhaji Dr. Aminu Ado Bayero, ya bukaci gwamnatin jahar, ta Kara Himma wajen gyaran tarbiyar matasa da kuma yin aiyukan sa za su kawo ci gaban Kano.
PRNigeria Hausa
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1254 days 18 hours 43 minutes 37 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1236 days 20 hours 25 minutes 2 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com