Wani rahoton tsaro na kamfanin Beacon Consulting ya bayyana cewa yawan mutanen da aka hallaka a Najeriya cikin watan Afrilun 2024 ya zarce na watan Maris da ya gabata da kimanin kaso 34.4 cikin ɗari.
Rahoton tsaron na wata-wata wanda da kamfanin ke fitarwa ya nuna cewa a cikin watan na Afrilu an kashe mutum 1,097 yayin da a watan Maris aka kashe mutum 816.
Hakan a cewar rahoton “abu ne mai ban tsaro”, tare da bukatar hukumomi su ɗauki matakan da suka dace wajen daƙile matsalolin tsaron da ke haifar da irin waɗannan kashe-kashe.
Jihar da aka fi kashe mutane a cikin watan na Afrilu ita ce Borno, inda aka kashe mutum 367, sai Zamfara mai biye mata a matsayi na biyu, inda aka kashe mutum 113, yayin da Kano ta zo a matsayi na uku, inda aka kashe mutum 64.
Borno ce jihar da ta fi shan wahala sanadiyyar matsalar hare-haren ƴan ƙungiyar Boko Haram.
Duk da cewa gwamnatin Najeriya ta yi ƙoƙari wajen rage ayyukan mayaƙan na Boko Haram amma har yanzu akan samu hare-hare nan da can.
Read Also:
Haka nan mayaƙan na Boko Haram kan dasa nakiyoyi a hanyoyin ababen hawa, wani abu da ke haifar da asarar rayuka.
A ɓangaren garkuwa da mutane domin karɓar kuɗin fansa kuwa jihar Zamfara ce a gaba, inda aka yi garkuwa da mutum 122, sai Borno a matsayi na biyu, inda aka yi garkuwa da mutum 40, yayin da jihar Delta take a matsayi na uku, inda aka sace mutum 29.
Zamfara na daga cikin jihohin da suka fi fama da matsalar ƴan bindiga masu garkuwa da mutane domin neman kuɗin fansa.
Ƴan bindigan na kai hare-hare a ƙauyuka, inda suke satar dukiya da mutane domin neman kuɗin fansa.
Duk da cewa gwamnati na cewa tana bakin ƙoƙarinta wajen magance matsalar amma har yanzu matsalar na ci gaba da haifar da asarar rayuka da tagayyara al’umma a faɗin jihohin arewa maso yammacin ƙasar.
Rahoton ya bayyana cewa an yi garkuwa da mutum 311 yayin da aka raunata mutum 342 a cikin watan na Afrilu a faɗin Najeriya.
Sai dai a ɓangare guda rahoton ya ce an samu raguwar yawan kai hare-hare da kuma sace-sacen al’umma domin neman kuɗin fansa.
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1254 days 21 hours 24 minutes 17 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1236 days 23 hours 5 minutes 42 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com