Babbar kotun tarayya a jihar kano ta bada umarnin dawo da sarkin Kano Muhammadu Sunusi kan karagar mulkin masarautar jihar.
Mai shari’a AM liman ne ya bayar da umarnin gaggauta dakatarwa ga gwamnatin jihar, bayan bayan wata kara da sarkin Dawaki Babba, Aminu Babba dan Agundi ya shigar gaban kotun.
Read Also:
Alhaji Aminu Babba Dan Agundi ya yi karar Rukunonin guda 8 da suka haɗar da Gwamnatin jihar kano, Majalisar dokokin jihar, Kakakin Majalisar dokokin jihar, Kwamishinan Shari’ar na Kano, Kwamishinan yan sandan jihar, Babban sufeton yan sandan Nigeria , Civil Defense, da kuma hukumar DSS.
Idan dai za’a iya tunawa Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya sanya hannu kan sabuwar dokar masarautun jihar ta 2024 bayan da majalisar dokoki ta soke dukkan masarautun jihar biyar da aka ƙirƙira a shekarar 2019.
Jim kaɗan bayan rattaba hannu a kan dokar, gwamnan ya sanar da naɗa Khalifa Muhammadu Sanusi II a matsayin sabon Sarkin Kano na 16, bayan ya sauke Aminu Ado Bayero daga kan kujerar.
Matakin kuma ya nuna cewa an soke masarautun Gaya da Bichi da Ƙaraye da kuma na Rano.
PRNigeria Hausa
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1254 days 12 hours 4 minutes 17 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1236 days 13 hours 45 minutes 42 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com