Ƴan bindiga sun hallaka akalla sojojin Najeriya biyar a wani harin ba-zata da suka kai a jihar Abia da ke Kudu maso gabashin Najeriya, yankin da ke fama da rikicin ƴan aware.
wannan dai na kunshe ne cikin wata sanarwa da sojojin suka fitar a yau Juma’a, mai dauke da sa hannun daraktan yaɗa labarai na rundunar sojin, Edward Buba. inda ta ce babu wata kungiya da ta ɗauki alhakin kai harin, sai dai sojojin sun dora alhakin hakan kan ƴan awaren da ke fafutukar kafa ƙasar Biafra.
Sanarwar ta ce sojoji za su mayar da martani kan hakan: “Za mu yi kokarin kawar da ƙungiyar gaba ɗaya.”
Read Also:
Najeriya na fama da rikice-rikice da suka hada da ƙungiyar ƴan awaren Biafra da ke ƙaddamar da hare-hare a Kudu maso gabas yayin da Arewa maso yamma ke fama da sace-sacen mutane domin neman kudin fansa, sai kuma arewa maso gabas da ta kwashe shekara 15 tana fuskantar rikicin Boko haram.
IPOB na fafutukar kafa ƙasar Biafra ta hanyar ficewa daga Najeriya, inda yawancin ƴan ƙungiyar ƙabilar Igbo ne tuni dai aka kama shugaban ƙungiyar Nnamdi Kanu, wanda ke da takardar shaidar zama ɗan Birtaniya a shekarar 2021 a Kenya, wanda yanzu haka ke fuskantar shari’a kan ta’addanci a Najeriya.
PRNigeria Hausa
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1254 days 21 hours 30 minutes 48 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1236 days 23 hours 12 minutes 13 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com