Majalisar dokokin kano ta mangantu kan jinkirin komawarta bakin aiki

Majalisar Dokokin jihar Kano ta musanta labarin dake cewa tayi jinkirin komawa aiki ne, saboda barazanar tsaron da take fuskanta akan dambarwar Masarautar jihar.
Kakakin Majalisar Dokokin Kano Rt, Honarabul Jibril Ismail Falgore ne ya sanar da hakan ta cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Kamaluddeen Sani Shawai ya aiko wa PRNigeria a safiyar Laraba, sanar ta ce wannan labarin bashi da tushe ballantana makama.
A cewar Falgore “wannan labari ne mai haɗari da wasu mutane ke yaɗawa wanda ke cewa, mun ƙi komawa zaman majalisa saboda barazanar tsaron da muke fuskanta akan dambarwar masarautar Kano ba gaskiya bane, domin kuwa babu wani labari makamancin wannan koma mai kama da shi”. inji Falgore.
Sanarwar ta kuma ayyana ranar 15 ga watan Yuli a matsayin ranar da zata dawo daga hutun da tayi, domin ci-gaba da samar da managartan ƙudirirrikan da zasu dace da manufofin Gwamnatin Kano, ƙarƙashin jagorancin Injiniya Abba Kabir Yusif na ciyar da Jihar gaba.
A ƙarshe sanarwar ta yi fatan al’umma zasuyi watsi da wancan labari da ake yaɗawa, kuma su ci-gaba da yin addu’oin samun zaman lafiya da kwanciyar hankali a lungu da saƙo na jihar.

PRNigeria Hausa

Kidnapped School Children

Yauri FGC Students, Kebbi
1189 days 15 hours 29 minutes 30 seconds,

Baptist School Students, Kaduna
1171 days 17 hours 10 minutes 55 seconds

Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Spent 88 days from May 30, 2021 - August 26, 2021


Report By: PRNigeria.com

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com