Home DUNIYA Kotu a Abuja ta dage saurarar karar da ake bukatar Ganduje ya...

Kotu a Abuja ta dage saurarar karar da ake bukatar Ganduje ya sauka daga shugabancin APC

Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja a Najeriya ta sake dage sauraren karar da ke neman a tsige tsohon gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje a matsayin shugaban jam’iyyar APC na kasar har zuwa ranar 5 ga watan Yuli.

Mai shari’a Inyang Ekwo, a ranar Laraba, ya dage ci gaba da zama sauraron karar a karo na biyu domin baiwa mai kara damar amsa sabuwar bukatar da Ganduje ya shigar na kalubalantar cancantar karar.

A zaman na Laraba, lauyan mai kara, Benjamin Davou, ya shaida wa kotun cewa Sanusi Musa, SAN, wanda ke kare Ganduje, ya mika masa wata sabuwar bukata.

Ya ce zai bukaci lokaci don yin nazari kan ko zai amsa takardar. Lauya Musa bai yi adawa da bukatar Davou na dage zaman ba.

A saboda haka mai shari’a Ekwo ya dage ci gaba da sauraron karar har sai ranar 5 ga watan Yuni domin ci gaba.

PRNigeria Hausa

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
HOTO: NSCDC ta Tsare Jami'ai 24 Kan Mutuwar Masu Hakar Ma'adinai a TsareShirin Tallafin Mai: Atiku ya yi Watsi da Gaskiyar Magana – APCGwamnatin Tarayya ta Inganta Samar da Abinci ta Hanyar Shirin AgriShield na ONSA Daga Chido OnumahAtiku ya yi Tambaya Kan Rashin Zuwa UNGA a Karo na Uku da Tinubu ya yi, ya Nemi Karin BayaniFalconets ta Fice Daga Gasar Cin Kofin Duniya ta Mata Ƴan Kasa da Shekaru 20 Bayan Colombia ta Sha Kashi a Wasan KarsheMatawalle Ya Nemi Tallafin Czech Don Samar da Alburusan DICON da Canja FasahaRundunar Sojojin Najeriya Ta Tallafa wa Iyalan Sojojin Gambia da Suka MutuFilato: Sojoji Sun Kama Masu Garkuwa 11, Sun Kwato MakamaiOPHK ta yi Bayani Kan Rahoton Amnesty na 2016 Dangane da Mutuwar da Ake Zargi a Barkin Giwa2027: Sama da Mambobin Jam'iyyar NDC 6,000 Sun Sauya Sheka Zuwa PDP a EnuguKwankwaso ya Nuna Aniyar Yin Sulhu da Gwamna YusufYadda Hon. Hudu Kanje Ya Sake Fasalin Jagorancin Cigaban Kasa Daga Mika'il Ja'afarƳan Sanda Sun Kama Mutane 300 a Farmakin Wuraren da Ake Aikata Laifuka a FCT Sun Kwace Wukake, Bindigar Wasa, da WiwiZakari Mohammed: Dole Kwara ta Cika Kwarewarta – Dan Takarar ADC ya Nemi Muhawara a BayyaneWSCIJ ta Yaba wa PRNigeria Kan Ci Gaba da Tallafawa Matasa Wajen Sadarwa Bayan Karewar Tallafi
X whatsapp