Rundunar ‘yan sandan jihar Yobe dake arewa maso gabashin Nijeriya ta tabbatar da kama Usman Garba mai kimanin shekaru 30 da take zargi da ayyukan garkuwa da mutane a jihar.
Kakakin rundunar, DSP Dungus Abdulkarim ne ya bayyana hakan, inda yace a ranar 5 ga watan Yunin shekarar 2024 da misalin karfe 1 na yamma, jami’ai daga sashen (SID) suka sami nasarar kama Usman Garba dan Asalin kauyen Katarko dake karamar hukumar Gujba, a kan hanyar sa ta zuwa kashe kason da ya samu a wata garkuwa da suka gudanar.
Read Also:
”Wanda ake zargin guda ne cikin mabobin wata tawaga da suka kware wajen fashi da makami, garkuwa da mutane domin karbar kudin fansa da kuma satar shanu a karamar hukumar hukumar Gujba da garuruwan dake makotaka da garin.
”Tawagar suke da alhakin garkuwar da akayi baya-bayannan a wani wurin zaman fulani da ake kira da Babaram Muktum a karamar hukumar ta Gujba, inda suka yi garkuwa tare da karbar kudin fansa naira miliyan 1 da dubu dari 6.
“sauran mambobin kungiyar sun tsere, amma rundunar na kokari domin tabbatar da ta kamasu.”
PRNigeria hausa
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1254 days 16 hours 4 minutes 11 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1236 days 17 hours 45 minutes 36 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com