Kungiyoyin kwadagon na NLC da TUC sun sake tabbatarwa da shugaban kasa Bola Tinubu matsayar su kan mafi karancin albashi naira 250,000.
Jaridar Politics Digest ta ruwaito Shugaban kungiyar na kasa Joe Ajaero ne ya bayyana hakan ga manema labarai jim kadan bayan ganawar su da shugaban kasar a fadar sa dake birnin tarayya Abuja, inda yace sun tsaya kai da fata kan mafi karancin albashin ma’aikatan.
Tinubu yace yana bukatar lokaci domin yin nazari gami da tuntubar masu ruwa da tsaki, kafin aika kudirin mafi karancin albashin ga majalisar kasa.
Read Also:
da yake ganawa da manema labaran a ranar alhamis Ajearo da wasu shuwagabannin kungiyoyin kwadago na kasar, yace shuwagannin kwadagon sun zo ne su tattauna ba daidaitawa ba.
inda yace ganawar zata cigaba mako na gaba.
bayan ganawar ta tsahon sa’a, shuwagabannin kungiyoyin kwadagon sun fito bisa rakiyar shugaban kasa, inda suka fadawa ‘yan jarida cewa zasu koma zuwa ga mutane kafin daga bisani su dawo fadar shugaban kasar.
Shugaban kungiyar YUC Festos Osifo, yace bayan sun gama bayyana matsayar ta su shima shugaban kasa yayi bayani, duk dai bai bayyana abin da Tinubun ya fada a yayin ganawar ba.
PRNigeria Hausa
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1254 days 16 hours 20 minutes 7 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1236 days 18 hours 1 minute 32 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com