Gwamnatin jihar Kano ta yi alƙawarin kammala aikin gyara dukkannin cibiyoyin koyar da sana,oin dogaro da Kai da kuma kirkire-kirkire Wanda tsohon Gwamna Rabi’u Musa kwankwaso ya Samar tun a shekarar 2011 a daukacin ƙananan hukumomi 44 da ke Kano.
Gwamna Alhaji Abba Kabir Yusuf ne ya bayyana hakan yayin bikin ranar baje kolin fasahar matasa ta duniya da cibiyar koyar da sana’o’i ta Aliko Dangote dake ƙaramar hukumar Dawakin kudu haɗin gwiwa da hukumar kula da ilimin ƙananan yara ta duniya UNESCO ta shirya.
Read Also:
Gwamnan ya ce yin riko da sana’o’in hannu zai taimaka wajen habaka tattalin arziki da Kuma samawa Matasa aikin yi.
Abba Kabir ya yi alkawarin samawa cibiyar da gidajen kwanan dalibai da biya musu kudin karatu da daukar nauyin kai su makaranta a kullum da kuma kulawa da walwalarsu.
Da ya ke jawabi a wajen taron karamin ministan ma’aikatar ci-gaban matasa Mista Ayodele Olawode ya yaba da harkokin cibiyar, inda ya ce ma’aikatar sa ta fito da wani shirin ilimantar da matasa miliyan 7 sana’o’in dogaro da kai.
Shugaban Hukumar UNESCO a Nijeriya Abdulrahman Diyalo ya ce za su yi haɗin gwiwa da gwamnatin kano da cibiyar koyar da sana’o’i ta Aliko Dangote domin koyar da dubban matasa sana’o’in dogaro da kai.
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1254 days 11 hours 59 minutes 24 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1236 days 13 hours 40 minutes 49 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com