Sojojin Nijeriya sun tura sako ga masu Shirin gudanar da Zanga – Zanga

Shalkwatar tsaron Najeriya ta gargaɗi masu shirin shirya zanga-zanga tsadar rayuwa a faɗin ƙasar da su guji jefa ƙasar cikin ruɗani.

Wannan na kunshe ta cikin wata sanarwa da daraktan yaɗa labaran ma’aikatar tsaron ƙasar, Manjo Janar Edward Buba ya fitar, inda ya ce duk da cewa ‘yan ƙasar na da ‘yancin gudanar da zanga-zangar, rundunar tsaron ƙasar ba za ta lamunci tayar da fitina a ƙasar ba.

Ya ce rundunar ta fahimci masu shirya zanga-zangar na yunƙurin kwaikwayar abin da ya faru a Kenya, inda zanga-zangar ta rikiɗe zuwa tashin hankali.

”Koda yake ‘yan Najeriya na da ‘yancin bayyana abin da ke damunsu, sojoji ba za su lamunci duk wani abu da zai iya janyo tashin hankali a ƙasar nan da sunan zanga-zanga ba”, in ji sanarwar.

Ya ƙara da cewa, sojojin sun bankaɗo shirin wasu ‘ɓata-gari’ da ke ƙoƙarin amfani da zanga-zangar wajen farmakar ‘yan ƙasar da ba su ji ba su gani ba.

“Yayin da ‘yan ƙasa ke da ‘yancin gudanar da zanga-zangar lumana, ba su da hujjar shirya wani abu da ka iya tayar da tarzoma ko aikata laifuka”, in ji Manjo Janar Buba.

“Mun dai ga abin da ya faru a Kenya, inda wasu ɓata-gari suka mayar da zanga-zangar lumana zuwa tashin hankali, wanda kuma aka kasa magancewa”, in ji shi.

Ya ce sojojin ƙasar sun sha zuwa ayyukan wanzar da zaman lafiya a ƙasashe makwabta musamman ƙarƙashin shirin samar da tsaro na yammacin Afirka, ECOMOG, kuma sun san yadda al’umomin ƙasashen ke faɗawa cikin mawuyacin hali sakamakon tashe-tashen hankulan, don haka ba su so hakan ta faru a Najeriya ba.

PRNigeria Hausa

Kidnapped School Children

Yauri FGC Students, Kebbi
1254 days 40 minutes 42 seconds,

Baptist School Students, Kaduna
1236 days 2 hours 22 minutes 8 seconds

Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Spent 88 days from May 30, 2021 - August 26, 2021


Report By: PRNigeria.com

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com