Tinubu ya sa hannu kan dokar mafi kankantar albashi ta naira dubu 70

Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya sa hannu kan dokar mafi ƙanƙantar albashi ta naira dubu 70,000.

Mai bai wa shugaban kasar shawara ta musamman kan al’amuran majalisar dattijai, Sanata Basheer Garba Lado ne ya tabbatar da matakin cikin wata sanarwar da ya fitar a birnin Abuja.

Matakin ya kawo ƙarshen watannin da aka shafe ana tattaunawa tsakanin hukumomi da ƴan ƙwadago da kuma ɓangaren masu kamfanoni.

Tinubu ya sa hannu kan dokar a fadarsa da ke Abuja kwanaki bayan da majalisar dokokin ƙasar ta miƙa masa ƙudirin.

Ya ce sa hannu kan dokar da shugaba Tinubu ya yi na nuna ya cika alƙawarin da ya yi wa ƴan ƙasa.

sanarwa tace “A yaƙin zaɓe, Tinubu ya yi alƙawarin inganta rayuwar ma’aikata kuma ya cika alƙawarin” in ji Lado.

Bai tsaya iya nan ba, ya tabbatar cewa an samar da dokar mafi ƙanƙantar albashi da yanzu ya zama dole a yi nazarin mafi ƙankantar albashin duk bayan shekara uku saɓanin shekara biyar.

Matakin dai ya zo ne yayin da wasu al’ummar Najeriya ke shirin gudanar da zanga-zanga don nuna takaicinsu kan tsadar rayuwa da taɓarɓarewar tattalin arziki.

PRNigeria Hausa

Kidnapped School Children

Yauri FGC Students, Kebbi
1254 days 16 hours 12 minutes 43 seconds,

Baptist School Students, Kaduna
1236 days 17 hours 54 minutes 8 seconds

Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Spent 88 days from May 30, 2021 - August 26, 2021


Report By: PRNigeria.com

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com