Kungiyar kare hakkin bil’adama ta Amnesty International a Najeriya ta nuna damuwa kan sabbin zarge-zargen taimaka wa ta’addanci da hukumomin kasar ke yi kan ƙungiyar ƙwadago ta NLC da shugabanninta.
A cikin wata takardar sanarwa da ta fitar, Amnesty ta soki yunkurin hukumomin gwamnati da cewa matakin da rundunar ƴansandan Najeriya ta ɗauka na gayyatar Joe Ajaero wani yunƙuri ne kawai na tursasa wa NLC ta yi abin da gwamnati ke so.
A ranar Talata ne wata sanarwa da rundunar ƴansanda ta Najeriya ta fitar ta buƙaci shugaban na NLC, Joe Ajaero ya bayyana a gabanta domin amsa tambayoyi kan wasu tuhume-tuhume da ake masa da suka shafi tallafa wa yunƙurin tayar da rikici a Najeriya.
Hakan na zuwa ne bayan wani samame da jami’an tsaro suka kai a hedikwatar ƙungiyar ta NLC, inda suka ce sun yi hakan ne a wani ɓangare na binciken da suke gudanarwa kan wani mai shirya tarzoma.
Amnesty International ta buƙaci hukumomin da su mutunta ƴancin ƙungiyoyin ƙwadago domin bayyana ra’ayoyinsu, ya kuma yi gargaɗin a guji amfani da ikon gwamnati wajen rufe bakin kungiyar ta NLC.
Amnesty International ta bayyana yadda ake samun karuwar cin zarafin ƙungiyar ƙwadagon a cikin shekarar da ta gabata, ciki har da harin da ƴansanda suka kai wa Ajaero a watan Nuwamba da wani samame da aka kai hedikwatar ta NLC a baya-bayan nan.
Kungiyar ta yi Allah-wadai da waɗannan ayyuka a matsayin katsalandan ga ƴancin kai na ƙungiyar ƙwadagon.
Amnesty ta kuma yi kira da a gaggauta kawo ƙarshen neman murƙushe shugabannin ƙungiyar ta NLC, tare da bayyana zargin da ake yi musu a matsayin maras tushe.
PRNigeria Hausa
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1254 days 19 hours 26 minutes 25 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1236 days 21 hours 7 minutes 50 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com