Rundunar ƴansandan Najeriya ta tabbatar da sakin ɗaliban nan 20 da ke karatun aikin likita, waɗanda aka sace a jihar Benue a ranar Juma’a ta makon da ya gabata.
A wata sanarwa da kakakin ƴansandan ƙasar, Muyiwa Adejobi, ya fitar ya ce a jiya Juma’a ne ofishin mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro, ya ceto ɗaliban da aka riƙe su a dajin Ntunkon, da ke ƙaramar hukumar ADO ta jihar Benue, ba tare da an biya wani kuɗi ba.
Tashar talabijin ta Channels, ta ce wata majiya da ta tabbatar da ingancinta, ta tabbatar mata cewa an yi amfani da wasu jiragen yaƙi masu sauƙar ungulu guda uku a aikin ceto ɗaliban, inda ta ce an kama wasu daga cikin masu garkuwar wasu kuma an kashe su.
A ranar Alhamis ta makon da ya gabata ne aka sace ɗaliban na jami’ar Maiduguri da jami’ar Jos tare da likitocin da suke tare da su a kan hanyarsu ta zuwa wani taro.
Ƴan kwanaki kaɗan bayan sace su, ƴan bindigar sun tuntuɓi iyalan ɗaliban suna son a ba su kuɗin fansa naira miliyan 50, kafin su sake su.
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1255 days 10 hours 19 minutes 2 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1237 days 12 hours 27 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com