Gwamnatin jihar Adamawa ta gargardi mutanen garuruwan dake fuskantar yuwuwar aukuwar ambaliyar ruwa gargadi da su gaggauta tashi su koma tudu domin kaucewa asarar rayuka da dukiya.
Babbar daraktan hukumar bada agajin gaggawa ta jihar (ADSEMA) Dr. Celine Laori ce ta yi gargadin a yayin da take ganawa da kamfanin dillanci labarai na NAN a garin Yola dake jihar.
Tace mammakon ruwan saman da ake makawa a kananan hukumomi uku da suka hadar da Madagali, Demsa, da kuma Numan sun isa izina ga mutanen da ke rayuwa a kwari ka iya fuskantar barazanar amfaliyar.
Laori ta kara da cewa ambaliyar ruwan ta shafi garuruwa 21 dake karkashin kananan hukumomi uku, wadda ta yi sanadiyyar mutuwar mutane shida tare da raba sama da 12,961.
“Ambaliyar ta shafi harkokin yau da kullum na mutane, ta lalata Gadoji, Gidaje, Shaguna, Wuraren kula da lafiya, Makarantu, Gonaki da sauransu.”
Read Also:
“A Madagali kadai, ambaliyar ta shafi mutane sama da 10,264 a garuruwa 11 wanda mutane ke cigaba da karbar kulawa a sansanoni tara mabambanta.
“A Numan, ta Shafi mutane 1,113 inda ta raba 206 da muhallin su a garuruwa biyar, wanda yanzu haka suke zaune a sansanoni 2, haka ma a Demsa ta shafi mutane 1,582 a garuruwa biyar.
Laori ta kara da cewa gwamnatin jihar ta dauki matakin gaggawa na samarwa wadanda iftila’in ya rutsa da su tallafin da ya hadar da na Abinci, da wadanda ba na ci ba, da suka hadar da Shinkafa, Maize, Man Gyada, Abin shinfida, bokita, Magani, kayan sawa na manay da na yara.
Daga bisani tayi kira ga sarakunana gargajiya da su yawa da kokarin gwamnati ta hanyar wayar da kan Al’umma don tseratar da rayukan su, ta kuma bukaci kungiyoyi masu zaman kansu da masu hannu da shuni da su tallafawa yunkurin Gwamnatin wajen samawa al’ummar da suka fada cikin iftila’in Abinci.
PRNigeria Hausa
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1254 days 18 hours 39 minutes 59 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1236 days 20 hours 21 minutes 24 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com