Wani harin mayakan boko haram kan masallata yayi sanadiyyar mutuwar mutane 34, a garuruwan Mafa, Tarmuwa dake jihar Yobe a arewa maso gabashin Nijeriya.
Mayakan na boko haram sun isa wani masallaci yayin da al’umma ke tsaka gudanar da sallah Magriba, in suka ka su da harbin kan mai uwa da wabi a ranar lahadin data gabata.
Mai sharhi kan al’amurarran da suka shafi tsaro a yankin tafkin Chadi Zagazola Makama, ya ruwaito cewa harin na matsayin martanin mayakan boko haram kan Al’ummar yankin bisa kin biyan harajin da suka yi ga kungiyar dake tayar da kayar bayan a yankin.
Read Also:
Yace aboye al’ummar garin na biyan mayakan na boko haram haraji ba tare da sanin jami’an tsaro ba, wannan ne yasa mayakn na boko haram kai musu mummunan harin da yayi sandiyyar mutuwar mutane.
Haka kuma rahoton yace a wani yunkuri na tsananta lamarin mayakan sun binne wasu abubuwan fashewa guda hudu akan hanya domin harar dakarun da zasu kawo dauki bayan sun kamala gudanar da ta’addancin kan Al’ummar.
Wannan harin na boko haram ya sake fito da matsin da suke kara fuskanta a wajen jami’an tsaro, tare da fito da bukatar dake akwai na sake bawa dakarun sojojin bayanan sirrin don dakile ayyukan ‘yan ta’addan.
PRNigeria Hausa
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1254 days 21 hours 57 minutes 51 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1236 days 23 hours 39 minutes 16 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com