Gamayyar marasa rinjaye a Majalisar Wakilan Nijeriya ta nemi a gaggauta janye ƙarin farashin man fetur da aka ƙara kwanan nan, saboda hakan zai ƙara wa ‘yan Najeriya wahala.
Sanarwar da shugabansu Kingsley Chinda ya fitar ta ce an kara wannan farashin ne ba tare da tuntubar masu ruwa da tsaki ba, ya saba wa ka’idojin gaskiya, da adalci da ya kamata su zama jagora a yanke irin wannan shawara mai tasiri ga rayuwar jama’a.
Read Also:
Sanarwar ta ƙara da cewa ƙarin farashin Man zai haifar da ƙarin matsalolin tattalin arziki da suka haɗa da tsadar sufuri, kayan abinci, da sauran muhimman kayayyaki, wanda zai ƙara jefa ƙarin iyalai cikin talauci.
Marasa rinjayen sun ce rashin tuntubar Majalisar Tarayya da sauran masu ruwa da tsaki game da wannan ƙarin ba daidai ba ne, yayin da suka gargadi gwamnati da ta yi tunani a kan halin da ƙasa ke ciki na rashin aikin yi, tsadar rayuwa, da rashin daidaito, domin wannan na iya haifar da tarzoma da ƙarin fitina a cikin ƙasa.
A ƙarshe, sun yi kira ga gwamnatin Tinubu da ta gaggauta yin gyara tare da neman hanyoyin da za su kawo sauyi a tattalin arzikin ƙasar ba tare da ƙara wa jama’a wahala ba.
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1254 days 21 hours 3 minutes 51 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1236 days 22 hours 45 minutes 16 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com