Ƙungiyar ƙasashen yammmacin nahiyar Afrika, ECOWAS ta caccaki hare-haren da ƴan ta’adda su ka kai babban birnin Mali, Bamako a ranar Talata.
A wata sanarwa, ECOWAS ta bayyana rashin jin daɗin ta a game da waɗannan hare-hare, waɗanda ta ce su na barazana ga zamn lafiyar yankin yammacin nahiyar Afrika.
Read Also:
Sanarwar ta kara da cewa Kungiyar ta na jaddada ƙudirinta a kan duk wani shiri da kawo zaman lafiya mai ɗorewa a yankin.
A ranar Talata ce aka kai wa birnin Bamako munanan hare-hare, waɗanda ƙungiyyar nan mai ikirarin jihadi da ke da alaƙa da Al-Qaeda ta ɗauki alhakin kaiwa. Har yanzu dai ba a bayyana adadin mutanen da waɗannan hare-hare su ka rutsa da su ba.
Birnin Bamako bai cika fuskantar hare-hare na masu ikirarin jihadi ba kamar yadda wasu sassan kasarke fuskanta kusan kullayaumin.
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1254 days 19 hours 20 minutes 43 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1236 days 21 hours 2 minutes 8 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com