Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya yi kira da dukkan masu ruwa da tsaki a jihar Edo da su tabbatar an martaba ƙuri’a da zaɓin mutanen Edo a zaɓen da za a yi gobe.
Tinubu ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma’a ta hannun mai magana da yawunsa, Bayo Onanuga.
“Shugaba Tinubu yana kira ga ƴan takara da jam’iyyu da magoya baya da su martaba tsarin dimokuraɗiyya da zaɓin mutane. Ya yi ammanar cewa mutanen za su yi zaɓi wanda suka ga ya dace da shugabantarsu,” kamar yadda sanarwar ta nuna.
Da yake kira ga Hukumar INEC da jami’an tsaro su kasance na kowa, Shugaba Tinubu ya ce dole kowane ɓangare ya gudanar da harkokinsa cikin lumana.
Tinubu ya nanata cewa domokuraɗiyya na cigaba ne idan akwai fahimtar juna da hakuri da kuma girmama tsarin ƙasa, inda ya ƙara da cewa INEC ta ɗauki alwashin gudanar da zaɓe sahihi.
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1255 days 41 minutes 22 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1237 days 2 hours 22 minutes 47 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com