Gwamnatin jihar Kano ta kulla alakar inganta tattalin arziki da ilimi da kasar India, a wani bangare na yunkurinta na inganta kyakkyawar alaka.
Wannan na cikin wata sanarwa da babban daraktan yada labaran Gwamnan jihar Kano Sunusi bature Dawakin Tofa ya aikewa PRNigeria a ranar juma’a.
Inda ta ce gwamnan jihar Kano Alhaji Abba kabir Yusuf, ya bayyana hakan ne a yayin da yake karbar bakuncin jakadan kasar ta india Excellency Shri G. Balasubramanian a fadar gwamnatin jihar.
Read Also:
Abba kabir ya bayyana cewa akwai kyakkyawar alaka tsakanin kasar India da jihar kano musamman a fannin Ilimi, Lafiya, Noma, kasuwanci da kuma kere-kere, wadda take bukatar aka mata karfi domin amfanin kasar ta India da kuma jihar Kano.
Ya kuma kara da cewa gwamnatin kano zata cigaba da hadin gwiwa da india domin kamala tashoshinta na samar da hasken wutar lantarki guda biyu da suka hadar da Tiga da Challawa, domin habaka kamfanoni da kuma cigaban tattalin arziki.
Tun da fari dai da yake jawabi wakilin kasar Indian Excellency Shri G. Balasubramanian ya yaba da kokarin gwamnan bisa samar da ayyukan cigaba da zai taimakawa al’ummar jihar.
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1239 days 16 hours 32 minutes 30 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1221 days 18 hours 13 minutes 55 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com