Shekara guda da fara yaƙi tsakanin Hamas da Isra’ila, ƙasar ta Yahudawa ta kashe ƴan jarida da ma’aikatan kafafen yada labarai da yawan su ya zarce yadda aka taɓa gani.
ta cikin wani jawabi da kungiyar kare hakkin ‘yan jaridu ta duniya CPJ tace tun da ta fara ajiyar bayanai a game da yan jarida da ake kashewa daga shekarar 1992 bata taba samun kamar na wannan yaki ba.
CPJ ta ce aƙalla yan jarida da ma’aikatan kafafen yaɗa labarai 128 ne suka mutu sakamakon hare-haren da Isra’ila ke kai wa Gaza, kuma daga cikinsu, biyu ne kawai za a ce babu hannun dakarun Isra’ila a mutuwarsu.
Ƙungiyar CPJ ta gano cewa da gangan Isra’ila ta kashe yan jarida aƙalla 5 saboda ayyukan da su ke gudanarwa, kuma tana ci gaba da bincike a game yiwuwar kisan wasu ƴan jarida 10 da gangan.
A ranar 7 ga watan Oktoban bara, ƴan jarida, ƴan asalin Isra’ila sun mutu sakamakon harin da mayaƙan Hamas su ka kai ƙasar, wanda ya haddasa yaƙin da ake ci gaba da yi a halin yanzu.
Read Also:
Kasashe-kashen da katsalandan a cikin aikin jarida, kame da kuma katse layukan intanet da lalata gidajen jarida da sauran su, sun haddasa tasgaro a aikin aikewa da rahotanni a ,game da abubuwan da ke faruwa a Gaza. Sai dai daga rana r 4 ga watan Oktoba, CPJ ta tabbbatar da wadannan cewa:
Daga cikin yan jarida 128 da aka kashe, 123 Falasɗinawa ne, sai ƴan Lebanon 3 da ƴan Isra’ila 2.
Kashi 11 na waɗanda aka kashe, mata ne,kuma akasarin ƴan jaridan da aka kashe ba su na ƙasa da shekaru 40 da haihuwa.
Hare-haen sama da Isra’ila ta kai ne su ka yi sanadin mutuwar Kashi 75 na Falasɗinawa ƴan jarida; sauran sun mutu ne sakamakon harbi da su ka hada da na jirage marasa matuƙa, tankokin yaƙi da sauransu.
Tun da aka fara yakin, an kama Falaɗinawa yan jarida 69; Isra’ila ta kame 66, sai makuntan Falasɗinu sun kama 3. Har yanzu akwai Falasdinawa yan jarida guda 43 da ke tsare a hannun mahukuntan Isra’ila.
An samu rahoton lalata gidajen jarida kimanin 70 a wannan yaƙin, kana Isra’ilar ta rufe wasu 5 har sai illa masha allahu.
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1254 days 11 hours 30 minutes 6 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1236 days 13 hours 11 minutes 31 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com