Tsohon shugaban majalisar dattawa ta ƙasa, Dr. Abubakar Bukola Saraki, ya ce tsohon gwamnan jihar Kano Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso kwararre ne wajen iya jagoranci.
Saraki ya bayyana haka ne a saƙon taya Kwankwaso murnar cika shekara 68 da haihuwa a yau 21-10-2020.
A cikin wata sanarwa da mataimakinsa a kan kafafen yada labarai, Abba Gwale ya fitar, Saraki, ya bayyana Kwankwaso a matsayin ɗan uwa kuma aboki wanda kuma ya kware wajen iya jagoranci.
Read Also:
“A yau da yake murnar zagayowar ranar haihuwarsa, ina taya iyalansa da ƴan uwansa da mabiyansa murnar wannan rana, sannan ina roƙon Allah ya ci gaba da ƙarfafa masa gwiwa, ya bashi cikakkiyar lafiya da basira da tsawon rai”. Inji Saraki.
Saraki da Kwankwaso dai sun yi aiki tare a majalisa ta takwas, a lokacin da Sarakin, wanda shima tsohon gwamnan jihar Kwara ne, yake matsayin shugaban majalisar dattawa daga shekara ta 2015 zuwa 2019, lokacin mulkin tsohon shugaban kasa Muhammad Buhari.
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1254 days 22 hours 15 minutes 6 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1236 days 23 hours 56 minutes 31 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com