Tinubu ya sallami ministoci biyar cikin kunshin ministocinsa

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya sallami ministoci biyar tare da naɗa wasu sababbi bakwai da kuma sauya wa goma ma’aikatu.

Wata sanarwa da fadar gwamnatin kasar ta fitar a shafinta na X, ta nuna cewa ministocin da aka cire sun hadar da Barr. Uju-Ken Ohanenye; ma’aikatar harkokin mata, Lola Ade-John; ministan harkokin yawon buɗe idanu, Farfesa Tahir Mamman; ministan ilimi, Abdullahi Muhammad Gwarzo; ƙaramin ministan gidaje da raya birane, Dr. Jamila Bio Ibrahim; ministar matasa.

Sai dai shugaba Bola Tinubu ya sauya wasu daga cikin ministocin ma’aikatu da suka hadar da Hon Dr. Yusuf Tanko Sununu; ƙaramin ministan ilimi ya koma ƙaramin ministan jinƙai da rage talauci, Dr. Morufu Olatunji Alausa; ƙaramin ministan lafiya, ya koma ministan ilimi, Barr. Bello Muhammad Goronyo, ƙaramin ministan ruwa da tsafta, ya zama ƙaramin ministan ayyuka, Hon. Abubakar Eshiokpekha Momoh, ministan raya Naija Delta, ya koma ma’aikatar raya yankuna (sabuwa), Uba Maigari Ahmadu, ƙaramin ministan ƙarafa ya koma ƙaramin ministan raya yankuna, Dr. Doris Uzoka-Anite, ministar masana’antu da kasuwanci da zuba jari ta koma ƙaramar ministar kuɗi, Sen. John Owan Enoh, ministan raya wasanni ya koma ƙaramin ministan kasuwanci da zuba jari (masana’antu), Imaan Sulaiman-Ibrahim, ƙaramar ministar harkokin ‘yansanda ta koma ministar mata, Ayodele Olawande, ƙaramin ministan matasa ya koma ministan raya matasa, Dr. Salako Iziaq Adekunle Adeboye, ƙaramin ministan muhalli, ya koma ƙaramin ministan lafiya.

shugaban kasar ya kuma nada sabbin ministocin da suka hadar da Dr Nentawe Yilwatda – Ministan ma’aikatar jinƙai da yaye talauci, Muhamamd Maigari Dingyaɗi – Ministan ƙwadago, Bianca Odinaka Odumegu-Ojukwu – Ƙaramar ministar harkokin waje, Dr Jumoke Oduwale – Ministar ma’aikatar kasuwanci da zuba jari, Idi Mukhtar Maiha – Ma’aikatar kusa da dabbobi, Hon Yusuf Abdullahi Ata – Ƙaramin ministan gidaje da raya birane, Suwaiba Said Ahmad phD – Ministar Ilimi.

Kidnapped School Children

Yauri FGC Students, Kebbi
1239 days 12 hours 34 minutes 25 seconds,

Baptist School Students, Kaduna
1221 days 14 hours 15 minutes 50 seconds

Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Spent 88 days from May 30, 2021 - August 26, 2021


Report By: PRNigeria.com

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com